Wani tsohon hadimi ga ministan tsaro na Najeriya, Bello Matawalle, ya fallasa muhimman bayanai na zargin ci gaba da mu’amala da manyan shugabannin ‘yan bindiga da kuma amfani da su wajen tilasta al’umma ta kuri’ar APC lokacin yana gwamna a Zamfara.
Wani rahoto na jaridar Sahara Reporters ya bayyana yadda tsohon gwamnan Zamfara kuma ministan tsaro na yanzu, Bello Matawalle, ke ci gaba da mu’amala kai tsaye da manyan shugabannin ‘yan bindiga a jihar. Wannan zargi ya fito daga wani tsohon mai ba shi shawara wanda aka boye sunansa saboda tsaro, inda ya bayyana cewa Matawalle ya rika ba ‘yan bindiga kuɗi, motoci har da siyasa yayin yana gwamna.
Rahoton ya ce, tsohon hadimin ya bayyana cewa,
Matawalle ya saya wa ‘yan bindiga shanu da suka sata a farashi mai sauƙi, musamman lokacin Sallah, inda yake sayan kowanne dabba kan Naira 150,000 kai tsaye daga hannunsu. Haka kuma, ‘yan bindigar sukan zo fadar gwamnatin jihar su tattauna da shi batutuwan siyasa da kuma hanyar da za su tilasta al’umma su kaɗa masa kuri’a a zaɓe.
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa Matawalle ya siyo sabbin motoci Hilux guda 36 ya miƙa wa shugabannin ‘yan bindiga.






