Kin taɓa sanin cewa kankana ba kawai kayan marmari bace, tana da gagarumin amfani ga lafiya da fata? Ga dalilin da yasa nake shan kankana kullum!
Kankana ba kawai kayan marmari bace—abinci ne mai ƙayatarwa, sirrin lafiya da kyau. Mata na son kyallin fata, ma’aurata na neman kuzari, kankana na da damar kawo duk wadannan. Idan kana son ƙara kuzari a soyayya, ko nutsuwa a fata, shan kankana na daga cikin matakan farko.
Kankana na ɗauke da sinadarai masu anfani kamar haka:
1. Ruwan Kankana Mai Yawa (92%):
Kankana na taimakawa wajen rage ƙishirwa da gajiya, musamman a lokacin zafi. Idan ka sha, jikinka zai samu ruwa yadda ya kamata.
2. Sinadarin Lycopene:
Wannan antioxidant yana kare zuciya, fata, da rage hatsarin kamuwa da cututtukan daji.
3. Vitamin C & A:
Sinadaran nan na ƙara ƙarfafawa ga garkuwar jiki da lafiyar ido, suna tsaftace fata da ƙara ingancin gani.
4. Potassium:
Yana taimakawa wajen daidaita hawan jini da inganta aikin zuciya, don kaucewa matsalolin jini.
5. Citrulline:
Wannan sinadari yana ƙarfafa lafiyar jijiyoyi da rage gajiya, musamman bayan motsa jiki.
6. Lafiyar Hanji:
Kankana na da fiber mai yawa, wanda ke saka kashi yayi laushi da kuma kara lafiyar hanji.
Saboda haka, shan kankana kullum ba kawai jin daɗi ke kawowa ba, har ma da kariya ga lafiya da kyawun fata. Bana kallon kankana a matsayin kayan marmari kawai, abinci ne mai aiki tamkar magani ga jiki da zuciya.
Tambaya:
Kai fa, kana ganin kankana nada amfani ko kawai kayan marmari ce ba tare da wani amfani ba?






