Rundunar ƴansandan Abuja ta fitar da sanarwa cewa babu gaskiya a labarin yunkurin kashe Laftanar Ahmed Yerima, sojan da ya samu sabani i da Ministan Abuja kwanan na.
Sanarwar da kakakin rundunar ƴansandan Abuja, SP Josephine Adeh, ya fito da ita ta bayyana cewa babu rahoton da ke tabbatar da an yi wani yunkuri na kashe Laftanar Ahmed Yerima, matashin sojan ruwa da ya yi hayaniya da Ministan Abuja, Nyesom Wike, a baya-bayan nan.
Rundunar ta yi kira ga jama’a da su daina yada labaran da ba su da tushe ko makama, saboda hakan ka iya tayar da hankalin al’umma.
idan za”a tuna a daren ranar lahadi ne, jaridar Vanguard, ta fitar da rahoton cewar wasu wadanda baá sani ba tare da kulle fuskokin su, sun kai wai Laftanar Yerima hari Abuja.
Ku cigaba da bibiyar wannan jaridar ta mu ta ArewaJazeera domin samun ingatattun labarai, nishadi da ma al’amuran yau da kullum.






