A rayuwar aure, ba kowane lokaci ne mijin ke da sha’awar jima’i ba, musamman idan rayuwa ta cika shi da aiki, damuwa, ko gajiya.
Wannan yasa wasu matan aure su kasa fahimtar yadda zasu motsa sha’awar mijinsu.
Ba wai dole ne mijinki ya fara nuna sha’awa ba, ke ma a matsayin mace za ki iya motsawa da tunzura shi ta hanyoyi masu hikima.
Ga wasu hanyoyi da zaki iya amfani da su:
1. Sakon Batsa da Hotunan Soyayya:
Ki tura masa sakonnin soyayya da hotuna masu nuni da kauna ko batsa tun kafin ya dawo gida, hakan yana sa zuciyarsa ta fara tunzura da sha’awa.
2. Shirya Abincin Da Yake Sha’awa:
Ki girka masa abinci ko shayi na musamman da kike sanin yana matuƙar so, domin hakan yana motsa hankalinsa da sha’awar kasancewa kusa da ke.
3. Motsa Bayanki da Kirjinki:
Ki yi shiga mai hankali da motsi mai laushi wanda zai rika tunzura sha’awarsa yayin kallonki.
4. Zauna Kusa da Shi:
Yayin da yake cin abinci, ki zauna kusa da shi, ki yi masa kwarkwasa da tabbatar masa babu wani damuwa a jikinki.
5. Sanar da Bukatunsa:
Ki tuna masa irin bukatuwarsa da zakuwa da kike yi masa a baya, hakan zai sa shi tunanin ki da sha’awarki.
6. Kwalliya da Adon Bacci:
Ki kawata kanki bayan wanka, ki yi kwalliya mai laushi, ki tabbatar jikin ki yana nuna shauki, zauna a gabansa, ki daura kafanki a cinyarsa idan ya dace.
7. Shafa Mai a Jikinki:
Ki bar shi ya shafa miki mai a wasu bangarorin jikinki musamman bayanki da duwawunki domin kara armashi.
8. Zauna Akan Cinyarsa:
Ki yi masa hiran soyayya yayin da kike zaune akan cinyarsa, ki shafa ko taɓa wasu bangarorin jikinsa.
9. Kawata Takin Kwanan Ku:
Ki tabbatar dakin kwanciyarku da gadonku suna cikin tsari da tsafta, domin yanayi mai kyau yana kara sha’awa.
10. Tausa da Sha’awa:
Ki sa shi yayi miki tausa yayin da kike tsirara a rufe dakinsa, wannan yana kara jin daɗi da natsuwa.
Wadannan matakai suna taimaka wa mace wajen karawa mijinta armashi da tunzura sha’awarsa, musamman ga maza masu lafiya.
Muhimmanci, wannan abu yana bukatar hikima, hakuri, da kulawa domin tabbatar da jin daɗin juna.
Allah Ya bada sa’a.
—






