Ba kowace soyayya ba ce take zuwa da gaskiya. Wasu mata suna shiga rayuwar namiji ne ba don soyayya ba, sai don abin da za su samu.
Idan ba ka lura ba, zaka iya kashe lokaci, kudi da zuciya a inda ba ka da daraja.
Saboda haka yana da muhimmanci ka gane alamomin da ke nuna mace tana anfani da kai kawai.
—
Alamomi 7 Na Mace Mai Amfani Da Kai
1. Tana tuntubarka ne kawai idan tana bukata
Idan ka lura tana kiranka ko chatting ne kawai idan tana da bukata (kudi, taimako, ko wani abu), wannan alama ce mai karfi.
—
2. Bata nuna kulawa ko damuwa da kai
Ba ta tambayar halin da kake ciki, lafiyarka ko yadda rayuwarka take tafiya.
> Soyayya ta gaskiya tana tare da kulawa.
—
3. Tana son kudi fiye da dangantaka
Idan kullum magana ta koma kan kudi, kyauta, ko abubuwan da zaka siya mata, to akwai matsala.
—
4. Bata saka effort a soyayyar
Kai ne kake kira, kai ne kake kula, kai ne komai. Ita bata bada wani kokari.
—
5. Tana bacewa idan baka bada abu ba
Da zarar ka rage bayarwa, sai ka ga ta fara nesa ko bata kula da kai.
—
6. Bata son haduwa da danginka ko abokanka
Idan tana gujewa duk wani abu da zai sa dangantakar ta zama serious, to akwai alama.
—
7. Tana da excuses a koda yaushe
Duk lokacin da kake bukatar ta, sai ka ji uzuri iri-iri.
—
> Abin Da Ya Kamata Ka Yi
Kada ka yi soyayya da ido rufe
Ka duba yadda take mu’amala da kai ba magana kadai ba
Kada ka bada kudi ko komai da wuri
Ka daraja kanka – idan baka da daraja a wurinta, ka ja baya
—
> Shawara Mai Muhimmanci
Soyayya ba kasuwanci ba ce. Idan mace tana son ka saboda abin da kake bayarwa kawai, da zarar ka daina bayarwa, soyayyar zata gushe.
> Ka nemi mace mai son ka saboda kai, ba saboda abin da kake da shi ba.
—
Sanin wace mace ce ta dace da kai zai taimaka maka ka guji ciwon zuciya da asarar lokaci.
Ka bude ido, ka saurari halayenta, kuma ka dauki mataki idan ka ga alamomin anfani.
—






