Wani magidanci ya dawo gida daga kasuwa, yana mai farin cikin ganin iyalansa.
Sai kuwa yaci karo da mahaifiyarsa a gida — ta zo ne domin ta duba jikokinta kamar yadda mahaifiya ke so ga ‘ya’yanta da jikoki.
Amma kafin ya zauna, sai ya ji muryar matarsa tana hayaniya— ta shiga cacar baki da mahaifiyarsa har lamarin ya kai ga zagi.
A cikin damuwa da takaici, magidancin yayi nufin sa baki ko daukar mataki kai tsaye.
Amma mahaifiyarsa cikin hikima da natsuwa ta dakatar da shi, tana rokon ya hakura kada ya tada gardama a wannan lokacin.
Magidancin yayi kamar ya hakura domin girmama mahaifiyarsa, ya bari ta koma gida bayan ta duba jikokinta.
Sai dai da mahaifiyar ta tafi, a yinin nan magidancin ya kasa jurewa, sai yayiwa matarsa dukan tsiya saboda rashin girmamawa da ta nuna wa mahaifiyarsa.
Wannan labari na koyar da mu muhimmancin hakuri, ladabi, da mutunta juna a cikin gida — musamman ga uwaye. Auren da ya samu girmamawa tsakanin dangi, cikin hakuri da juriya, shi yafi dorewa da kawo zaman lafiya ga kowa.






