Shi wannan yanayin Jima’i mata suna yinsa haka nan maza ma suna son shi. Sai dai yadda masu aure suke nasu ya bambamta da na mazinata.
Akwai lokacin da namiji yake dawowa cikin sha’awa, ko kuma bayan ya shigo yaga matarsa a cikin wani yanayin da zai ji kawai yana sha’awar ta. Haka nan suma mata suna samun kansu a irin wannan lokacin duk da dai maza sun fi samun gamsuwa a irin wannan Jima’i fiye da mata.
GARGADI: Wannan Labari Na Ma’aurata Ne Kawai 8+~ Karin Ilimi Ne Da Koyarwa, ba Batsa Muke Yadawa Ba Anan.
Shi yanayin wannan Jima’i da mai sha’awar da wanda bai da duk ba shirye suke ba, kawai yana zuwa musu ne a nan take inda guda zai kamu da sha’awar guda kuma ya nemi nan take ya biya bukatar tasa.
Akwai yanayin da namiji zai samu matarsa a dakin girki na zamani tayi shigar zamani kawai sai yaji sha’awar ta ya kamashi, nan take sai ya turmushe ta. Haka nan mace zata samu mijinta yana zaune ko yana bacci kawai taji tana bukatarsa nan take zata soma lalubansa yana tashi har ta afka masa. Nasan ma’aurata kadai zasu fahimci abunda nake bayani anan.
A takaice shi Jima’i na kwantar da sha’awa ga ma’aurata abu ne wanda yake bijirowa guda daga cikinsu nan take a lokacin kuma zai nemi motsawa guda sha’awar nasa koda kuwa bai da ita domin neman hadin kan a samu a kwantar da sha’awa.
Ma’aurata da suka gwada irin wannan Jima’i na bazata, dayawa a cikinsu sun nuna jin dadin Jima’i, wanda wasu har ya zame musu dabi’a. Duk kuwa da mata ba saifai suke samu gamsuwa a irin wannan Jima’i ba, amma kuma hakan na samar musu da jin dadin Jima’i ba tare da zuwan kai ba, kuma suna kara jin kaunar mazajensu.
Tabbas shi wannan Jima’i bazata na kwantar da sha’awa, ba a bukatar wani shiri na musamman kaman yadda Jima’i na neman haihuwa yake bukata. Wata ma ko wanka bata yi ba lokacin da mijin zai bukace ta, haka nan mazan wani lokacin daga dawowa aiki wajen cire kaya mace ke zarcewa, ko namiji ya dawo gida da rana cin abinci matarsa ta ce sai yayi zai fita.
Yanada kyau ma’aurata su rika baiwa juna hadin kai a duk lokacin da guda sha’awar sa ta motsa yake neman biyan bukata ba tare da hanawa ko jan rai ba. Domin sha’awa kanta halitta ce, dole ne a duk lokacin data motsa so take a motsa, don haka hanawa guda biyan wannan bukatar zai iya cutar da guda har su tsinci kansu inda bai dace ba. Sai dai fa ko a irin wannan Jima’i mace na iya samun ciki, sai dai manufar yi a kwantar da sha’awa ne ba domin neman haihuwa ba.
Yadda Ake Jima’in Kwantar Da Sha’awa Cikin Mintuna – Bisa Koyarwar Musulunci
A addinin Musulunci, dangantakar jima’i tsakanin miji da mata abin ibada ne mai girma. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kuma a cikin jima’in dayanku akwai sadaka.” (Muslim)
Wannan rubutu zai koya maka hanyoyin da suka dace na kwantar da sha’awa tare da gamsar da matarka cikin ladabi.
1. Addu’a Kafin Jima’i
Kafin fara komai, yi wannan addu’ar:
“Bismillahi, Allahumma jannibna ash-shaitan, wa jannib ash-shaitana ma razaqtana”
(Da sunan Allah, Ya Allah ka nisantar da mu daga Shaidan, kuma ka nisantar da Shaidan daga abin da ka azurta mu)
2. Muqaddama (Foreplay) – Mabudin Nasara
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kada dayanku ya auku kan matarsa kamar dabba, a samu manzo tsakaninsu.” Suka ce: “Mene ne manzon?” Ya ce: “Sumba da kyakkyawan magana.”
Abubuwan da za a yi:
- Kyakkyawan magana mai daɗi
- Sumba da shafawa
- Nuna soyayya da tausayi
- Ba da lokaci – kada a yi gaggawa
3. Sanin Wuraren Da’a na Mace
Allah Ya halicci mace da wurare masu taushi. Miji mai hikima zai koyi:
- Sauraro da lura da martanin matarsa
- Tambayarta abin da take so
- Nuna haƙuri da tausayi
4. Kwantar da Sha’awa – Hanyoyi Masu Amfani
a) Numfashi mai zurfi – yana taimakawa wajen sarrafa jiki
b) Rage gudu – idan ka ji kusa, tsaya dan lokaci
c) Canza matsayi – wannan yana taimakawa
d) Mayar da hankali kan matarka – maimakon kanka kawai
e) Yin zikiri a zuciya – yana taimakawa wajen natsuwa
5. Bayan Jima’i
- Ku yi wanka tare ko daban
- Ku ci abinci ko sha ruwa tare
- Ku yi magana mai daɗi
- Ku gode wa Allah
Kammalawa
Jima’i a Musulunci ba kawai sha’awa ba ne – ibada ce da ke ƙarfafa dangantaka. Idan aka yi ta da ladabi, tausayi, da niyyar ibada, zai zama abin da ke kusantar da ku ga Allah da kuma ga junanku.
Wallahu A’alam (Allah ne Mafi sani)






