a Shida Season 2 Episode 7: Rikicin Gado, Soyayya, da Satar Jama’a
Sabuwar fitowar shirin “Wata Shida” ta zo da nishadi, tashin hankali da abubuwan da suka fi karfin tunani. Kalli yadda Kawu Nakowa ke matsawa Zarah kan rabon gadonsu, yayin da Ameerah ke hannun ‘yan fashi!
A cikin wannan sabuwar Episode 7 na Season 2, shirin “Wata Shida” na ci gaba da jan hankali.
Kawu Nakowa ya dage wajen matsawa Zarah lallai sai an raba gadon mahaifinta, wanda shi Kawu ke da hannu ciki.
Zarah, a cikin rudani da matsaloli, ta shiga auren bogi da Dahiru—wanda shi kuma yana sonta da gaske, ba kamar yadda take tunani ba. Rikicin soyayya da na gida ya dauki sabon salo!
A gefe guda kuma, har yanzu yar Kawu Nakowa, wato Ameerah, tana hannun masu garkuwa da mutane tare da Lailu, saurayin ta mai ɗan kai da kai. Rashin tabbas da rudani yana kara kamari a gidan Nakowa.
Duba cikakken bidiyon domin ganin yadda zullumi da rudani ke ci gaba, da kuma irin yadda kowa zai fuskanci matsalolinsa!
Kalla Bidiyo A Kasa!






