Mutane da yawa suna shiga soyayya da zuciya ɗaya, amma suna fita da ciwo da damuwa.
Ba wai saboda soyayya bata da kyau ba ne, sai dai saboda rashin fahimtar wasu muhimman abubuwa.
Idan ka fahimci waɗannan abubuwa guda 3, rayuwar soyayyarka za ta sauya gaba ɗaya.
—
1. Ba Kowa Aka Nufa Da Kai Ba
Ba duk wanda kake so ba ne ya dace da kai.
Wasu mutane darasi ne, ba makoma ba
Wasu suna zuwa ne domin su koya maka abu
Kada ka tilasta soyayya inda babu haɗin zuciya
👉 Fahimta: Rashin dacewa ba gazawa ba ne.
—
2. Darajarka Ba Ta Dogara Da Wani Ba
Mutane da yawa suna rasa kansu saboda soyayya.
Kada ka rage darajarka domin ka faranta wa wani rai
Kada ka nemi kulawa ta hanyar roƙo
Ka fara son kanka kafin ka nemi wani ya so ka
👉 Mutumin da ya san darajarsa, ba a wasa da shi.
—
3. Soyayya Ba Kalamai Kawai Ba Ce — Aiki Ne
Magana mai daɗi ba ta wadatar.
Duba yadda yake mu’amala da kai
Duba yadda yake kula da kai
Duba consistency ɗinsa
👉 Aiki ya fi magana gaskiya.
—
Soyayya ba ta da wahala idan ka fahimce ta da kyau.
👉 Ka tuna:
Ba duk wanda kake so ne zai so ka ba…
Amma wanda ya dace da kai, ba zai sa ka wahala ba.
—






