Wanene Isa Pilot? Tarihin Isa Sunusi Bayero, Basarake Kuma Matukin Jirgin Sama na Kano



Alhaji Isa Sunusi Bayero, wanda aka fi sani da “Isa Pilot,” sananne ne a Kano da Najeriya baki ɗaya. Shi ɗan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi I ne, wanda ya mulki daga 1954 zuwa 1963, kuma shi Kawu ne na Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Isa Pilot ya yi aiki a matsayin matukin jirgin sama mai zaman kansa, ya kuma tuka manyan shugabannin Najeriya biyar: Ibrahim Babangida, Sani Abacha, Olusegun Obasanjo, Abdulsalami Abubakar, da Ernest Shonekan. Daga baya ya koma zama sakataren sirri na marigayi Sarkin Kano Ado Bayero na tsawon shekaru 15.

Bayan rasuwar Ado Bayero, Isa Pilot ya ci gaba da aiki da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin sakataren sirri. Sai dai a shekarar 2017 aka kore shi daga wannan mukami, bisa zargin fitar da bayanan sirri daga masarauta, wanda hakan ya janyo bincike kan kashe kudade. Daga baya kuma wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai masa hari a gidansa da ke Kano.

Kirari da lakabi sun mamaye Isa Pilot a cikin al’ummar Kano,

kamar:

  • Zanga-zanga Uban Sunusi na II
  • Isa Ɗan Maryamu
  • Isa Zancen Sarki
  • Baƙar Fura dakan ibilisai
  • Wazirin Sarkin Aljanu
  • Isa rabi mutum rabi aljan
  • Ka tuka mota a ƙasa, ka tuka jirgi a sama
  • Zanga-zanga jikan Dabo

Ana masa lakabi da:
Mai Sarki, Zancen Sarki, Wazirin Sarkin Aljanu, Isah Pilot Zancen Sarki, Kawun Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, kuma ɗan’uwan Galadiman Kano Abbas Sunusi Bayero.

Isa Pilot mutum ne da tarihin rayuwarsa ke ɗaukar hankali da girmamawa a Arewa, musamman a fagen masarauta da tarihinta.


Hashtags:

#isahpilot #isahdanmaryamu #isahzancensarki #tarihi #kano #kanohistory #nigerianroyalty #arewacelebrity #kannywood #hausablog #sarautankano #waneneisapilot


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *