Wannan bayani na ma’aurata ne kawai.
Ba wai muna yaɗa batsa bane, muna yaɗa ilimi da hanyoyin ƙarfafa soyayya, kusanci da jin daɗin aure ne bisa ladabi.
Uwargida, ki matso kusa domin ga wani haɗin ganye da wasu mata ke amfani da shi don ƙara jin daɗi, kuzari da natsuwa a zamantakewar aure.
Ana amfani da:
Ganyen idon zakara
Minannas
A haɗa su a dafa su sosai. Bayan sun dahu, a tace ruwan, sannan a saka ɗan sugar lump ko zuma a sha.
Mata da dama sun shaida cewa:
yana taimakawa jiki ya samu natsuwa
yana ƙara kuzari
yana sa mace ta fi jin daɗin kusanci da mijinta
yana rage gajiya da bushewar jiki
Wannan ba magani ne na cuta ba, amma hanyar ƙarfafa jiki da jin daɗin aure ne ta hanyar halitta.
Mafi muhimmanci shi ne:
kulawa
tsafta
tattaunawa tsakanin ma’aurata
da fahimtar juna
Waɗannan su ne ginshiƙan jin daɗin aure.
Gargadi Mai Muhimmanci
Wannan bayani:
Na ma’aurata ne kawai
Ba koyar da batsa muke yi ba
Muna yaɗa ilimi ne domin inganta aure, soyayya da lafiya
Idan kina da wata matsalar lafiya, ki tuntubi likita.






