ArewaJazeera
  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home
Monday, March 2, 2026
  • Login
No Result
View All Result
No Result
View All Result
ArewaJazeera
No Result
View All Result
Home Hausa News

Tinubu Ya Tura Shettima Zuwa Kebbi Domin Jajantawa da Daukar Mataki Kan Sace Yan Matan Maga

Malamar Aji by Malamar Aji
November 18, 2025
in Hausa News
0
Tinubu Ya Tura Shettima Zuwa Kebbi Domin Jajantawa da Daukar Mataki Kan Sace Yan Matan Maga

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika Mataimakinsa, Kashim Shettima, zuwa Jihar Kebbi domin jajantawa al’ummar jihar da iyayen ’yan matan da aka sace a Maga. Shugaban ya tabbatar da tsauraran matakai don dawo da tsaro da kwato yaran cikin gaggawa.

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya sha alwashin cewa gwamnatin sa na kan kokari don kubutar da ’yan matan da aka sace daga makarantar sakandaren Maga a Jihar Kebbi.

Tinubu ya tura Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, domin jajantawa iyayen ’yan matan da kuma al’ummar Jihar Kebbi, tare da tabbatar da cewa gwamnati na aiki tukuru don dawo da tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya.

A cikin sanarwar mai ba shugaban ƙasa shawara kan labarai, Bayo Onanuga, an ce shugaba Tinubu ya jajanta wa rundunar sojin Najeriya bisa rasuwar sojoji da Birgediya Janar Musa Uba a Jihar Borno.

Shugaban ya nuna matukar damuwa da faruwar lamarin, tare da yin Allah-wadai da harin ta’addanci.

Ya bukaci al’umma, musamman a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro, da su rika ba hukumomin tsaro bayanan sirri don taimaka musu wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Tinubu ya jaddada cewa hukumomin tsaro ba za su iya yin aiki yadda ya kamata ba tare da goyon baya da bayanai daga al’ummar yankuna ba.

Related Posts

Kalla Bidiyo: ‘Yan Matan Da ‘Yan Bindiga   Suka Sace Tsakanin Sokoto da Zamfara
Hausa News

Kalla Bidiyo: ‘Yan Matan Da ‘Yan Bindiga Suka Sace Tsakanin Sokoto da Zamfara

February 24, 2026
Maryam Yahaya Ta Jawo Cece-Kuce a TikTok Bayan Tayi Live Dauke da Jariri A Hannu
Hausa News

Maryam Yahaya Ta Jawo Cece-Kuce a TikTok Bayan Tayi Live Dauke da Jariri A Hannu

February 23, 2026
Idan Kana Son Zama Mai Kuɗi, Dole Ka Sadaukar Da Waɗannan Abubuwa 10
Hausa News

Idan Kana Son Zama Mai Kuɗi, Dole Ka Sadaukar Da Waɗannan Abubuwa 10

February 21, 2026
Ana Zargin Maryam Yahaya da Amfani da Magungunan Ƙara Girman Jiki
Hausa News

Ana Zargin Maryam Yahaya da Amfani da Magungunan Ƙara Girman Jiki

February 17, 2026
Ango Ya Saki Amarya Saboda Rashin Nono — Darasi Ga Masu Shirin Aure
Hausa News

Ango Ya Saki Amarya Saboda Rashin Nono — Darasi Ga Masu Shirin Aure

February 17, 2026
“Nakan ji kunyar shiga mutane saboda manyan nonuwana”
Hausa News

Abubuwa 5 Da Namiji Zai Duba Kafin Ya Amince Wa Mace

February 16, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home

© 2025 ArewaJazeera.com

No Result
View All Result
  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home

© 2025 ArewaJazeera.com

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In