Wasu ma’auratan suna taba juna ne kawai idan suna son wani abu (jima’i). Wannan ba soyayya ba ce – cinikayya ce. Soyayya ta gaskiya ita ce rike hannun juna ba tare da wani dalili ba, da kuma rungumar juna kawai don nuna kauna.
Ku taba abokan zaman ku ba tare da wani dalili na musamman ba.
Ke mace, zauna a cinyarsa. Kai kuma maigida, shafa fuskarta, hannayenta kwarai kuwa, cigaba da shafa mata duwawu. Kada ku jira sai kun shiga dakin kwana.
Ku rika taba juna kullum, cikin wasa da kauna. Taba juna ba kawai don fara saduwa ba ne hadin gwiwa ne na zukata.
Ku kasance masu yawan taba juna da gangan. Taba juna magani ne.
Ku rungumi juna a kicin. Ku yi sumbata a hanyar corridor. Ku rike hannun juna yayin kallon talabijin. Wannan yana karfafa dankon zumunci, kuma ta hakan ne soyayya ke dorewa. Nuna kauna ta zahiri tana gina natsuwa a zuciya.
Idan kun je gado, kada ku kwanta kamar baki. Ku hada kafafunku, ku rike hannun juna, ku rungumi juna sosai.
Idan jiki ya dumu, zuciya ma za ta dumu. Abokin zamanka ba matashin kai ba ne da za ka jefar gefe guda nisanta jiki da juna yana iya raba zukata.
Taba juna yana nufin, “Ina nan tare da kai.” Yana sanyaya rai, yana kwantar da hankali, kuma yana hada zumunci.
Ba za ka iya gina kusanci na kwarai ba tare da taba juna ba. Ku cigaba da taba juna – kowace rana, a hankali, da kuma cikin wasa. Ka taba su, masoyi.
Ta hakan ne soyayya ke numfashi.






