Kwankwaso ya jaddada cewa Sunusi Lamido ne kawai Sarki a Kano, yana kiran sauran sarakunan a matsayin na bogi, lamarin da ya jawo wata sabuwa muhawara a jihar.
Tsohon Gwamnan Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana a fili cewa Sunusi Lamido ne kadai halastaccen Sarkin Kano, duk wani mai kiran kansa Sarki a yanzu toh shidai na bogi ne.
Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a wajen bikin yaye daliban Jami’ar Skyline da ke Kano, inda ya jaddada cewa mutanen Kano su dinga ganin Sunusi Lamido a matsayin Sarki.
Wannan kalaman Kwankwaso na ci gaba da janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta da gidajen labarai, musamman na ganin yadda dambarwar sarauta ke ci gaba da jan hankali a jihar Kano.






