Babban Lauya, Farfesa Sebastine Hon, ya bayyana cewa halin da Jami’in Sojan Ruwa A.M. Yerima ya nuna a rikicinsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sabawa doka da ka’ida
Babban Lauya mai daraja ta kasa (SAN), Farfesa Sebastine, ya bayyana cewa Jami’in Sojan Ruwa, A.M. Yerima, ya karya doka wajen rikicin da ya faru tsakaninsa da Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Wannan rikici ya auku ne lokacin da Minista Wike ya ziyarci wani fili da ake takaddama a ciki, inda ya nemi dakatar da aikin da ake yi, amma Yerima ya yi kokarin hana hakan da hujjar umarnin da ya samu daga manyan.
Farfesa ya jaddada cewa, duk da cewa Yaren Ministan ya yi tsauri, matakin da Wike ya dauka yana bisa doka da ka’ida. Ita kuwa dabi’ar da A.M. Yerima ya nuna, ta saba dokar aiki ta soja da ta kasa baki daya.
Ku cigaba da bibiyar jaridar Arewa Jazeera don samun ingantattun labarai da rahotanni na gaskiya.

Leave a Reply