Yawancin mata na daukar sit bath sai haihuwa kawai, amma sit bath na dauke da fa’idodi da dama ga lafiyar mace, ko bata haihu ba.
Sit bath wani nau’in wanka ne da mace zata zauna a cikin ruwan dumi na mintuna kadan.
Yana magance damuwa da radadi a wajen gaba, rage kaikayi, da kiyaye tsafta.
Wasu mata na zaton sai an haihu akeyin da sit bath, amma gaskiya sit bath na da matukar fa’ida:
- Tsaftar gaba: Yana taimakawa cire datti, magance wari da kaikayi.
- Rage radadi: Idan mace na fama da radadin gaba ko kumburi, sit bath na saukaka.
- Inganta lafiyar fata: Yana taimakawa rage kumburi da kaikayi ga fata.
- Ba sai haihuwa ba: Mata da ba su haihu ba ma za su iya amfani da sit bath don tsafta da nishadi.
To ku daina daukar sit bath a matsayin sai haihuwa akeyi, mata duka na amfana da shi!






