Tun bayan bikin auren jaruma Rahama Sadau da sabon angonta watanni baya, magoya baya da masu nazari sun dade suna jiran ganin fuskar mijinta.
Amma Rahama ta zabi kare sirrinta, ta boye fuskar angon har zuwa yanzu. Wannan sirri ya ƙara jan sha’awar masoya da yan Kannywood, musamman bayan fitowar bidiyo daga birnin Paris inda jaruma ke rayuwa cikin annashuwa da sabon angonta.
Bidiyon ya nuna Rahama da mijinta suna yawo a wuraren tarihi cikin birnin Paris, washe-washen fuska da murmushi, duk da fuskar angon har yanzu ta ɓoye. Wannan ya kara rikita kafafen sada zumunta, inda jama’a ke tofa albarkacin baki, suna tambaya “wanene sabon angon Rahama Sadau?”
Rahama Sadau dai ta shahara da ji daɗin rayuwa, salon kasaita da zama jagora a Kannywood. Wannan bidiyo ya kara tabbatar da farin ciki da zaman lafiya a gidanta, ya nuna soyayya da girmamawa a tsakaninsu, koda kuwa duniya bata gan fuskar mijin ba!
A cewar masoya da abokanta: “Soyayya ta gaskiya bama a buƙatar a nuna komai, farin ciki da zaman lafiya sun isa shaida.”





