Farji yana da wari na dabi’a. Amma wani lokaci warin yana canzawa ko ya yi tsanani. Menene ke haddasa hakan? Rashin tsafta ne, cuta, ko halitta? Wannan labari zai bayyana muku.
Shi farji yana da dan wari nasa ta dabi’a. Wannan al’ada ce.
Abin da ke zama matsala shi ne idan:
- Warin ya canza
- Warin ya yi tsanani
- Warin ya zama kamar na kifi
Abubuwan Da Ke Haddasa Warin Farji
1. Rashin Tsafta
- Rashin wanka akai-akai
- Rashin canza pant
- Amfani da sabulu ko turare mai karfi wanda yake lalata daidaituwar farji
2. Yawan Zufa
- Sanya kaya masassu da ba sa shan iska
- Zama a wuri mai zafi
3. Cututtuka (Infection)
- Bacterial vaginosis
- Infection na yeast
- Cututtukan da ake ɗauka ta hanyar saduwa (STIs)
4. Al’ada (Period)
- Jinin al’ada yana da wari
- Idan ba a canza pad lokaci-lokaci ba, warin zai kama farji
5. Abinci Da Dabi’u
- Cin wasu abinci
- Shan taba
- Rashin shan ruwa sosai
Duk waɗannan na iya canza warin farji.
6. Halitta
Wani lokacin warin kawai halittar mace ce. Kowane farji yana da wari nasa.
Abin Lura
Idan warin ya yi tsanani ko ya zama kamar warin kifi, hakan na iya nuna akwai infection. Ya kamata a ga likita nan take.
Yadda Za Ki Rage Warin Farji
Tsafta:
- Ki yi wanka akai-akai da ruwa kadai ko sabulu mai laushi
- Ki canza pant na cotton akalla sau biyu a rana
- Ki guji pant da ya matse sosai
- Ki yi shaving na gashin gaba
Abinci Da Sha:
- Ki sha ruwa mai yawa don tsaftace jiki
- Ki ci abinci mai kyau kamar yogurt (yana taimaka wa good bacteria a farji)
- Ki rage shan sugar da caffeine da yawa
Abubuwan Da Za Ki Guji:
- Turare ko sinadarai masu karfi a ciki ko wajen farji
- Zama da pad ko pant jikekke na dogon lokaci
- Sabulu masu karfi
Magungunan Gargajiya*
- Shafa ruwan Aloe Vera
- Shan ruwan kananfari
- Sarki da dan ruwan gishiri
- Yin sitbath da ruwan ganyen Neem
- Yin sitbath da ruwan ganyen magarya
- Yin tsarki ko sitbath da ruwan dumi da ma’uqal
- Shan shayin hulba
- Cin fruits da yawa
Lokacin Da Ya Kamata Ki Ga Likita
- Warin ya zama kamar na kifi
- Akwai ciwon farji ko kaikayi
- Akwai fitar ruwa mai launi dabam
- Warin bai tafi ba duk da tsafta
Kammalawa
Warin farji al’ada ce a wasu lokuta. Amma idan ya yi tsanani ko ya canza, akwai dalili. Na iya zama rashin tsafta, cuta, ko abinci. Ki kula da tsaftar jikinki, ki ci abinci mai kyau, ki sha ruwa. Idan matsalar ta ci gaba, ki ga likita.






