Tun kusan shekaru goma, ba a ga fuskar Adam A Zango a finafinan Saira Movies ba. Wannan ya biyo bayan sabani tsakanin shahararren jarumi da mai kamfanin, Aminu Saira. Shin menene ya janyo rabuwa?
A baya, kusan duk wani babban fim da kamfanin Saira Movies ke fitarwa, Adam A Zango shine tauraron da ke jagorantar fim din.
Darakta Aminu Saira bai da wani jarumi da ya fi Adam A Zango daraja a lokacin, saboda finafinai da dama da suka hada har da fitattun shirye-shirye masu armashi.
Amma a cikin kusan shekaru goma da suka gabata, ba a sake ganin Adam Zango a kowane finafinan Saira ba.
Bincike ya nuna cewa rashin ganin Zango a shirye-shiryen Saira ya biyo bayan sabani da ya faru tsakaninsa da Aminu Saira, musamman dangane da fim din “Dan Marayan Zaki”.
Asalin Adam A Zango ne jarumin shirin, sai dai ya ki halartar dandalin daukar fim din, wanda a karshe ya sa dole aka maye gurbinsa da Sadiq Sani Sadiq.
Wannan lamari ya sa kusanci da hadin kai tsakanin Adam A Zango da Aminu Saira ya ja baya, har zuwa yanzu ba a sake saka Adam a duk wani fim na Saira Movies ba.






