Sadaki ɗaya ne kawai daga cikin sharuɗɗan aure guda huɗu. Ba a ɗaura aure sai an ambace shi ko kwatankwacinsa.
Amma ai hankali: Bayar da sadaki kaɗai ba ya nufin aure ya ɗauru. Koda an yi baiko, baiko yarjejeniya ce kawai – ba aure ba.
Gaskiyar Da Yakamata Ku Sani:
Mace ba ta halatta ga namiji har sai an zauna an ɗaura musu aure a gaban shaidu.
Tunda ba a ɗaura muku aure ba, sunanku a idon Shari’a shi ne “saurayi da budurwa” – ba ma’aurata ba.
Idan wata mu’amala ta auratayya ta shiga tsakaninku kafin ɗaurin aure, sunan wannan abu a fili yake: ZINA. Laifin yana kan ku biyu, ga kuma zubewar darajarku a wajen Allah Maɗaukakin Sarki.
Gargaɗi Ga ‘Yan Mata:
Yanzu haka akwai wasu samari da suka mayar da sadaki ya zama “Ticket” na samun damar yin abin da ba daidai ba. Ta wannan dabara mummuna, sun ɓata rayuwar ‘yan mata da yawa.
Ku riƙe wannan:
- Bai halatta saurayi ya taɓa ko farcen yatsanki ba
- Ko da rana ɗaya ce ta rage kafin ɗaurin aure
- Ko da miliyoyin kuɗi ne ya kawo gidanku
Mutuncinki a hannunki yake. Ki kiyaye shi.






