Saduwa da iyali, kamar sauran ayyukan yau da kullum, na bukatar motsa sassan jiki.
Wannan ba kawai aiki ne na jima’i ba, amma yana daga cikin ayyukan da ke buƙatar ƙarin kuzari daga jiki gaba ɗaya.
Lokacin saduwa, sassan jiki da yawa suna aiki tare:
Huhu da numfashi – bugun zuciya da numfashi suna ƙaruwa.
Jijiyoyi da tsokoki – suna aiki don tabbatar da motsi da jin daɗi.
Ƙwaƙwalwa – tana da hannu wajen fahimtar motsin jiki da jin daɗi.
Saboda haka, saduwa ba kawai nishaɗi bane, aiki ne mai buƙatar kuzari da juriyar jiki gaba ɗaya.
Mafita don inganta kuzari
Bunƙasa kuzarin jiki ta hanyar motsa jiki ko atisaye akai-akai shi ne hanya mafi lafiya da inganci.
Shan magani ko ƙarin kuzari na wucin gadi yana iya tirsasa jiki yin aiki da ba zai iya ba, wanda hakan na iya kawo haɗari ga lafiyar jiki.
Bincike ya nuna cewa:
Motsa jiki akai-akai na ƙara kuzarin jiki gaba ɗaya.
Hakan na taimakawa wajen magance matsalolin saduwa da iyali.
Haka nan yana ƙara ƙarfin zuciya, huhu da tsokoki.
Shawara
Zaɓi lafiyarka, kuma ka zaɓi hanyar da ta dace:
motsa jiki akai-akai zai baka damar jin daɗin saduwa da iyali cikin lafiya da kuzari.
Wannan hanya ce mai dorewa fiye da dogaro da magunguna.






