Shirin Labarina ya kunshi jarumai masu fasaha, daga ciki akwai Agolan Baba Dan Audu da mahaifiyarsa. Abin mamaki, shekaru da suka bayyana a fim sun fi na gaske bambanci!
Maryam Aliyu Obaje wacce akafi sani da Madam Korede, ita ce mahaifiyar Agola, wato matar Baba Dan Audu, a cikin shirin Labarina. Sai dai idan akayi kididdiga a zahiri, Agola zai iya girmamata da kimanin shekaru 10. A wata hirar da akayi da Agola, ya tabbatar da cewa yana da fiye da shekara 40—tunda tun kusan 1998/1999 yake taka rawa a fagen fim.
Babu shakka, namiji na da alfarma; Agola a fim ya ke kamar bai wuce shekaru 25 ba, yayin da mahaifiyarsa take kamar ta lashe shekaru 60. Wannan yasa ake mamakin gaske.
shin da gaske Agola ya bawa Madam Korede shekara 10 da haihuwa?

Leave a Reply