Sau da dama, ana ganin matashi ya fi jin daɗi da natsuwa idan yana soyayya da bazawara. Shin me yasa hakan ke faruwa? Ga dalilai da hikimar soyayya da auren bazawara.
Ba duka maza ke son budurwa ba – wasu sun fi son mace da aka gina ta da ƙwarewa da natsuwa.
Bazawara mace ce mai hikima, haƙuri, da sanin darajar zaman lafiya a cikin gida.
Ta san dariyar aure da kukansa, kuma ta fahimci yadda za a zauna lafiya da mijinta.
Wasu matasa na gudun bazawara saboda maganar mutane, amma mai hangen nesa ya san kimarta fiye da surutu.
Idan namiji ya auri bazawara, yana samun abokiyar gaskiya, uwa mai taushi, da mace mai kwarewa a jindadin gida. Wannan gata ne da ba kowa ke ganewa ba.
Bugu da kari, Annabi (SAW) ya fi aurar da bazawara fiye da budurwa, don darajar da ke tattare da su. Jarumta ce ta namiji mai hankali da ba ya tsaya kan maganar jama’a, ya zabi aure da mace mai natsuwa da fahimta.
Soyayya da bazawara ta kunshi hikima, natsuwa da soyayya mai dorewa. Wanda ya zabi bazawara jarumi ne mai hangen nesa da zuciya mai mutunci. Zama lafiya ba surutu ba ne; natsuwa da sanin daraja na kawo farin ciki mai dorewa.






