Maza da dama suna son ci gaba da saduwa da matansu bayan zuwan-kai na farko, amma wasu suna ɗaukar lokaci mai tsawo kafin su sake samun kuzari, wasu kuma har awa 24 ko fiye.
Akwai mazan da ke iya yin zuwan-kai har sau biyar ba tare da sun sauka daga kan matansu ba. Bincike ya nuna cewa kashi 30 cikin 100 na maza suna da irin wannan halitta.
Kamar yadda ake samun irin wannan halitta a maza, haka ma akwai mata da ke bukatar lokaci mai tsawo kafin su sake jin sha’awa. Wasu mata na iya gamsuwa sau ɗaya kawai, wasu kuma suna bukatar zuwan-kai sau da yawa kafin su gamsu.
Duk masu irin wannan halitta ba su da wata matsala, sai dai kawai haka halittarsu take. Lokacin da suka matsa kansu su yi fiye da abinda jikin su zai iya ɗauka, suna iya cutar da kansu.
Bisa al’ada, bayan zuwan-kai, mutum yana bukatar mintuna 10 zuwa 20 na hutu domin gabansa ya samu damar sake maido da kuzari.
Sabbin ma’aurata na iya ɗaukar lokaci mai tsawo kafin su sake samun kuzari saboda rashin saba, amma da zaran sun saba, lokacin zai ragu.
Ga wadanda suke jinkiri kafin su sake mikewa bayan zuwan-kai, wannan na iya nuna raunin gaba ne, kuma ya kamata su tuntubi likita don neman taimako.
Rashin samun kuzari nan take ba yana nufin rashin lafiya bane ko rashin ƙarfin jini, abin halitta ne.
YADDA ZAKA YI TAZARCE…
Akwai dabaru da yawa ga maza da ke son yin tazarce bayan zuwan-kai na farko. Wasu na amfani da kwayoyi don ƙara ƙarfin jiki, amma akwai hanyoyi masu sauƙi da za su taimaka ba tare da magani ba.
Kafin maigida ya yi tunanin komawa ga matarsa karo na biyu, ya kamata ya tabbatar cewa tana da sha’awar hakan, domin hakan zai ba shi damar yin shirin komawa.
Hanyoyi Uku Don Ci Gaba Da Jima’i Bayan Zuwan-Kai:
- Kada Ka Fita Daga Jikin Matar Ka:
Ka bar gabanka a cikin nata na ɗan lokaci kadan bayan zuwan-kai. Wannan yana taimaka wa maigida da matar wajen ci gaba da jin daɗi.
- Ci Gaba Da Wasanni Da Juna:
Idan kuna da sha’awa, ku ci gaba da wasanni da juna bayan zuwan-kai. Wannan zai taimaka wajen dawo da kuzari cikin sauri. - Tsarki Da Ruwan Dumi:
Bayan zuwan-kai, wanke gabanka da ruwan dumi, da kuma kasan mararka kafin ka fita daga toilet, zai taimaka wajen dawo da kuzari.
Wannan shawarwari na taimaka wa maza su samu kuzari da jin daɗi a rayuwar aure.
Ka raba wannan labarin domin sauran maza su amfana!






