ArewaJazeera
  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home
Monday, March 2, 2026
  • Login
No Result
View All Result
No Result
View All Result
ArewaJazeera
No Result
View All Result
Home Zamantakewa

Me Yake Sa Ruwan Maniyyin Da Namiji Ke Kawowa Yake Tsinkewa ya zama ruwa-ruwa?

Malamar Aji by Malamar Aji
December 30, 2025
in Zamantakewa
2
Me Yake Sa Ruwan Maniyyin Da Namiji Ke Kawowa Yake Tsinkewa ya zama ruwa-ruwa?

Wannan na daga cikin tambayoyin da ake yawan yi mana.

Idan a can baya sperm ko maniyyin namiji ya na da kauri sai daga baya ya koma ruwa ruwa ko ya tsinke, akwai abubuwan da ke sa haka kuma In Shaa Allah ana iya magance su.

Rashin maganin waɗannan matsalolin yadda ya kamata na iya sa namiji ya zama ba ya haihuwa.

Abubuwan da ke sa ruwan maniyyin namiji tsinkewa ya zama ruwa ruwa

1. Yawan jima’i: Idan mutum yana jima’i sosai kuma bai bada lokacin da ruwan maniyyi zai sake taruwa a marar sa, toh ruwan maniyyi din zai fito ruwa ruwa a lokacin da yake kawowa.

2. Yawan istimnai: Wannan ya na sa ruwan maniyyin namiji ya yi ruwa ruwa kamar yadda yawan jima’i ke iya kawo wannan matsala.

3. Cututtukan infections: Kamuwa da cutar sanyin maran namiji shi ma yana sa sperm ya tsinke ko ya fara wari.

4. Ƙarancin sinadarinln zinc a jikin namiji na sa ruwan maniyyin sa ya yi ruwa ruwa. Idan a ka sha magani ana iya maye gurbin sinadarin na zinc da yake a cikin jini, saboda haka ana warkewa.

5. Ƙarancin kwayar halittar sperm din ya na sa maniyyin ya yi ruwa ruwa, ma’ana ƙarancin halittun haihuwa a cikin ruwan maniyyi oligospermia, ko azoospermia.

6. Wasu maza musamman matasa basu san banbanci tsakanin maniyyi da maziyyi ba. Wannan ya na saka hankalin su ya tashi a lokacin da suka fitar da maziyyi sai su ɗauka cewa maniyyin su ne ya tsinke ya koma ruwa ruwa.

Tests da ake yi domin bincikar tsinkewar ruwan maniyyiAna yin gwajin seminal fluid analysis (SFA) domin gane lafiyar ruwan maniyyi da kuma halittun haihuwa da ke cikin sa.

Wannan test din yana buƙatar namiji ya daina jima’i na aƙalla kwanaki uku sannan yaje dakin gwaji ya bada ruwan maniyyin sa domin aunawa.

Abubuwa guda uku su ne muhimman abubuwan da ake dubawa a cikin SFA:

1. Sperm count: Wannan shi ne adadin yawan ƙwayoyin halittun haihuwa da ke a cikin ruwan maniyyi.

Idan adadin su ya kasa kai ga yanda ake so, shi ke nuna oligospermia, kuma wannan na iya zama dalilin ruwan maniyyin mutum yayi ruwa ruwa ko ya tsinke. Kuma wannan na hana samun ciki.

2. Sperm motility: ma’ana motsi ko gudun ƙwayoyin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi.

Idan ya kasance ƙwayoyin sperm din adadin su ko yawan su daidai ne amma kuma basa motsi ko gudu yanda ya kamata ana samun matsala, wannan ma yana iya zama dalilin rashin haihuwa.

3. Sperm shape: ma’ana yanayin halittun ƙwayoyin haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi.

Ko wane ƙwayar halitta ana buƙatar ya zamo yana da kai, gangar jiki da kuma bindi. Idan Alal misali basu da halitta mai kyau ba za su kaiwa ga wurin da zasu haɗu da ƙwan mace domin a samu ciki.

Yadda ake inganta lafiyar maniyyin namiji

1. Rage damuwa: A lokacin da mutum ke ƙoƙarin gamsar da iyali tare da samun juna biyu a na son namiji ya zamo cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

2. A guji zafi: Musamman zafin da zai iya shafar mara kai tsaye. Yawan zafi ya na rage lafiya da ingancin ƙwayoyin halittan da ke cikin ruwan maniyyi, haka kuma yana hana musu girma.

3. A nisanci mu’amala da wasu chemicals dayawa irin magungunan kashe ƙwari ko haƙo ma’adanai.

4. A rage kasance wa cikin damuwa da tashin hankali da rashin samun isasshen hutu.

5. A kasance da matsakaicin nauyi, ma’ana nauyi madaiddaici. Ka da namiji ya zamo mai rama sosai ko mai ƙiba dayawa.

6. A rage shan giya ko a daina baki ɗaya

7. A daina shan miyagun ƙwayoyi, sigari da abubuwan da ke saka maye.

Latsa Nan Don Samun Wasu Sirrikan Soyayya Da Aure

Tags: #CiwoLokacinSaduwa #LafiyarJiki #Shawarwari #RayuwarAure #SaduwaMaiDadi #AmaryaDaAngo#Saduwa #Shaawa #RayuwarAure #Soyayya #Jindaɗi #Shawarwari #ZamanLafiyaWani magidanci dan Zaria ya samu kudi don sayen gida

Related Posts

Wannan Abu 3 Idan Ka Fahimta, Ba Zaka Sake Shan Wahala A Soyayya Ba
Zamantakewa

Alamomin Mace Mai Bin Maza (Ba Tare Da Kunya Ba)

March 2, 2026
Idan Mace Tana Soyayya Da Maza Biyu, Ga Alamomi 7 da Za Ka Iya Gani
Zamantakewa

Idan Mace Tana Soyayya Da Maza Biyu, Ga Alamomi 7 da Za Ka Iya Gani

March 2, 2026
‘Ya’yan Itatuwa 4 da Jikinka Ke Bukata Kowane Mako a Matsayin Namiji
Zamantakewa

‘Ya’yan Itatuwa 4 da Jikinka Ke Bukata Kowane Mako a Matsayin Namiji

March 2, 2026
Alamomin Da Za Su Iya Nuna Mace Na Sha’awar Mata (Lesbian)
Zamantakewa

Alamomin Da Za Su Iya Nuna Mace Na Sha’awar Mata (Lesbian)

March 1, 2026
Idan Sabon Aure Ya Haifar da Zafi Lokacin Fara Saduwa: Ga Abin da Ya Kamata a Yi
Zamantakewa

Nau’o’in Mazaje 8 Da Mata Ba Sa Saurin Barinsu

March 1, 2026
Alamomin Budurwa Mai Istimna’i (Masturbation)
Zamantakewa

Alamomin Budurwa Mai Istimna’i (Masturbation)

March 1, 2026

Comments 2

  1. IBRAHIM GARBA says:
    2 months ago

    Nil

    Reply
  2. IBRAHIM GARBA says:
    2 months ago

    I need

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home

© 2025 ArewaJazeera.com

No Result
View All Result
  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home

© 2025 ArewaJazeera.com

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In