Karancin jini (Anemia) yana faruwa ne idan jiki baya da isasshen hemoglobin ko ƙwayoyin jini ja da zasu ɗauki iskar oxygen zuwa sassan jiki.
Mata sun fi maza fuskantar wannan matsala saboda jinin haila, ciki da shayarwa.
🔹 Babban Abubuwan Da Ke Haddasa Karancin Jini Ga Mata
- Zubar jini mai yawa a haila
Idan mace na yin haila mai yawa ko tsawon lokaci, tana rasa ƙarfe (iron) da yawa fiye da yadda jiki ke maye gurbinsa. - Rashin cin abinci mai ƙarfe
Abincin da bai ƙunshi:
naman ja
hanta
kifi
wake
ganye masu duhu
yana sa jiki kasa samar da isasshen jini. - Ciki da shayarwa
Lokacin ciki da shayarwa, jiki na bukatar ƙarin jini domin jariri. Idan ba a ƙara abinci mai ƙarfe ba, anemia na faruwa. - Tsutsotsi a ciki
Tsutsotsi na shan jinin jiki a boye, suna jawo anemia ba tare da mace ta sani ba. - Ciwon mahaifa ko fibroid
Wadannan na iya jawo zubar jini da yawa a haila ko bayan aure. - Rashin sinadaran Vitamin
Musamman:
Vitamin B12
Folic acid
suna da matuƙar muhimmanci wajen gina jini.
🧍♀️ Alamomin Karancin Jini Ga Mata
Gajiya sosai
Jiri ko ciwon kai
Fari ko rawayar fata
Bugun zuciya da sauri
Faduwar gashi
Jin sanyi da kasala
Rashin sha’awar jima’i
🥗 Abincin Da Ke Kara Jini
Hanta
Kwai
Kifi
Ganyen alayyahu (spinach)
Wake
Gyada
Dabino
Tumatir + lemun tsami (yana taimaka wa iron ya shiga jiki)
🩺 Yaushe Zaki Ga Likita?
Idan kina:
yin haila mai yawa
gajiya kullum
jiri ko faduwar numfashi
yana da kyau ki je gwajin jini.
📝 Kammalawa
Karancin jini ba ƙaramin abu ba ne, yana shafar:
lafiyar mace
ciki
aure
kuzari da jin daɗin rayuwa
Da wuri mace ta kula da jinin jikinta, da wuri rayuwa ta inganta







Comments 1