Tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Reno Omokri, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya bayyana ra’ayinsa game da batun sadaki a cikin al’umma, musamman a al’adun Afirka.
A wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter), Omokri ya bayyana cewa asalin sadaki a al’adun Afirka da na Yahudawa na nufin kuɗin da namiji ke biya wa iyayen budurwa a matsayin girmamawa da alamar ɗaukar nauyin aure.
Ya ce wannan al’ada tana da tushe tun a cikin Littafi Mai Tsarki, inda ya ambaci Fitowa 22:17 a matsayin hujja.
Omokri ya yi bayani dalla-dalla kan bambancin “sadaki” da “kayan aure”, inda ya ce:
Sadaki dukiya ce ko kuɗi da ango ke biya domin auren budurwa.
Kayan aure kuwa dukiyar iyaye ce da suke bai wa ’yarsu domin ta fara rayuwar aure.
A cewarsa, abin damuwa shi ne yadda wasu al’ummomin Afirka ke buƙatar sadaki mai tsada daga mata da ba budurwa ba, yana mai cewa hakan ya kauce daga ainihin ma’anar al’ada, kuma ya zama wata hanya ta tilastawa mutane biyan kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
Omokri ya kuma jaddada cewa, a cewarsa, kalmar “amarya” a cikin Littafi Mai Tsarki tana nufin budurwa ne kawai, yana kawo hujjoji da misalai domin kare wannan matsayi. Ya ce wannan fahimta ce da ya kamata mutane su yi nazari a kanta, maimakon bin al’adu ba tare da tambaya ba.
A ƙarshe, Reno Omokri ya yi kira ga al’umma da su fahimci asalin al’adunsu da tushen aurensu, yana mai cewa salon aure da ake kira “na fararen fata” ba asalin al’adar Afirka ba ce.
A cewarsa, rashin fahimtar wadannan abubuwa na iya haifar da ruɗani da matsaloli a tarbiyya da zaman aure.






