A lokacin da aka zo kacaccala masarautar Kano, Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano na 16, ya bayyana muhimmancin tarihin al’ummar Bichi—inda ya jaddada cewa Bichi asalin Ƙasar Dagaci ce kawai ƙarƙashin Hakimin Tofa.
Mai martaba Sarkin Kano na, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa da yadda aka raba masarautar Kano, inda ya ce: “Lokacin da aka zo kacaccala masarautar Kano, mun bada shawara cewa ko za’a yi, kar a ɗauko wajen da basu da tarihin sarauta a basu, domin mutane suna mantawa cewa Bichi ƙasar Dagaci ce, ƙarƙashin Hakimin Tofa.”
Sanusi II ya jaddada cewa tarihin sarauta ya kamata a mutunta, inda kowane yanki ya san matsayinsa na masarauta da asalinsa.
A cewarsa, Bichi ba ta da tarihin masarauta irin ta Kano, sai dai asalin ta ƙasar Dagaci ce mai dogon mulki ƙarƙashin hakimai.
Maganar Sanusi II ta jawo tattaunawa kan yadda ake sauya tsarin masarautu a yankin Kano, da dalilan da ya sa ya ke kira a girmama tarihi da gadon sarauta.






