
Abul-Fatahi yaci gyaran Sheikh Gurumtum a kowacce gaba na muhadarar daya gabatar sannan kuma yace in aka samu mas’alah irin wannan ya bar masu ilimi suyi magana akai, Duba kurakuran
Wani shahararren malamin addini ya rushe duk wata hujja da mallam Ahmad Tijjani Gurumtum ya kawo yayin da yake bawa Mallam Lawan Triumph kariya akan wata mas’alah da ake zargin shi akai, inda ya tabbatarwa da duniya duk cewa duk zagaye kawai malamin yai tayi ya kasa kafa hujja da hadisi ko kuma zancen malamai ko daya.
Abul-Fatahi yaci gyaran Sheikh Gurumtum a kowacce gaba na muhadarar daya gabatar sannan kuma yace in aka samu mas’alah irin wannan ya bar masu ilimi suyi magana akai, saboda shi ba malamin hadisi ko fiquhu bane ko tafsiri shi malamin tiktok ne da Kuma status.
Malamin ya kara da cewar ko kusa jawaban Guruntum babu ilimi a ciki, hakan ma sake bayyana rashin karatun shi yayi da kuma karancin research.
Allah Ya Hada Kan Malaman Mu… Aamin
Leave a Reply