Binciken kimiyya ya tabbatar cewa farjin mace na iya tashi kamar na maza. Karanta wannan labari don fahimtar gaskiyar jikin mace da yadda wannan ilimi zai taimaka wa ma’aurata.
Yawancin mutane suna tunanin cewa tashi na jiki abu ne da ya kebanci maza kawai. Amma binciken kimiyya na zamani ya nuna wani abu mai ban mamaki – mata ma suna da irin wannan yanayi.
Farjin mace yana dauke da wani sashe da ake kira “clitoris” wanda yake da jijiyoyi sama da dubu takwas. Wannan adadi ya fi na mazaje. Lokacin da mata suka ji dadin jima’i, jini yakan taru a wannan yanki, kuma sai ya kumbura ya yi tauri kamar yadda al’aura ta maza take yi.
Masana ilimin jikin dan Adam sun bayyana cewa a lokacin da jariri yake cikin mahaifa, dukkan yara suna farawa da siffa iri daya. Sai daga baya hormones ke raba su zuwa namiji ko ta mace. Saboda haka, sassan jiki da yawa suna da kamanceceniya a tsakanin jinsi biyu.
Wannan ilimi yana da muhimmanci musamman ga ma’aurata. Fahimtar yadda jikin juna yake aiki zai taimaka wajen inganta dangantaka da kuma gamsar da juna.
Likitoci sun ce wannan yanayi na al’ada ne kuma lafiya ce. Babu abin kunya a ciki, domin haka ne Allah ya halicci jikin mutum.






