Dogaro da maula, wato jiran taimako daga wasu ba tare da kokari ba, na iya wa rayuwar mutum illa da dama. Ka gina yau da gobenka ta hanyar kokari, ka daina jiran na wani.
- Wulakanci: Mutane za su rage darajar ka, su dauke ka ba mai amfani.
- Raini: Za su raina ka, su saba da kai cikin rainin hankali.
- Jinkiri: Za ka tsaya wuri guda, ba za ka nemi ci gaba ba.
- Kishin-kai mara kyau: Za ka fara jin haushin wadanda ba su taimaka maka ba.
- Ƙuntataccen tunani: Za ka daina amfani da basira ko ganin damarka.
- Dogaro da mutane, mantawa da Allah: Za ka fi dogaro da mutane fiye da neman taimakon Allah.
- Rashin ci gaba: Ba za ka nemi damarka da kanka ba, ci gabanka zai tsaya.
- Bacin rai: Idan ba a taimaka maka ba, sai ka ji damuwa da rashin natsuwa.
- Asarar abokai: Ƙoƙarin roƙo-roƙo kullum yana gundurar abokai, har su rabu da kai.
Ka taimake kanka da iyalinka, Allah zai taimaka maka. Sana’a da kai da kokari tafi dogaro da maula






