Kalmar kirki guda daya na iya sauya ran mace, ta karfafa soyayya da zumunci a gida. Ga kalmomi guda 10 da suke faranta rai, amma mafi yawan maza suna boye su!
Ga jerin kalmomi 10 da zaka iya faɗa wa matarka, budurwarka ko uwar gidanka—kowane lokaci don ƙarfafa kauna:
- “Kin yi kyau sosai.” – Yabon sura yana kai zuciya nesa.
- “Ke ce burina a rayuwa.” – Kalmar jin dadin rayuwa.
- “Ina alfahari da ke.” – Kara burin mace ta ji darajarta.
- “Allah ya yi ki kyakkyawa, ciki da waje.” – Soyayya ta halitta da halayya.
- “Ke ce tauraron zuciyata.” – Ita mai haskaka rayuwa.
- “Ni ba zan iya rayuwa ba sai da ke.” – Murna da jin dadi.
- “Kin fi kowa birge ni.” – Yabawa da birgewa.
- “Duk lokacin da na gan ki, zuciyata tana bugawa da farin ciki.” – Tasirin kasancewa mace.
- “Ina son halayenki da yadda kike tafiyar da komai da nutsuwa.” – Son halaye da hikima.
- “Ke abar so ce, abar alfahari ce, abar koyi ce.” – Kara ƙarfafa mace.
Yawaita yabawa ba wai kan sura ba ke ba mace farin ciki —har da tunani, hali, ƙoƙari, da basira.
Magana daga zuciya ce ke da tasiri!
Fadakar da zuciya da ƙarfin soyayya shi ne ginshiƙin auren dake zama dindindin.
Kada ku manta cigaba da bibiyar Arewa Jazeera don labarai, nishaɗi, da ilimi—sirrin ma’aurata da tarihinsu!






