Shahararren mawakin siyasa, Dr. Dauda Kahutu Rarara, ya baje kolin farin ciki tare da ’ya’yansa yayin da suka ringa wasa a filin kwallo dake cikin gidansa, suna nishadantarwa da burgewa.
Sanannen mawakin siyasa, Dr. Dauda Kahutu Rarara, wanda aka fi sani da jami’ar waka, ya wallafa bidiyo a shafinsa na Instagram, inda aka hango shi tare da ’ya’yansa suna nishadi a filin kwallo na gida. Bidiyon ya nuna yadda suka ke cike da farin ciki yayin da suke wasa, abin burgewa da ban sha’awa ga duk mai kallo. Wannan ya karawa magoya baya da masoyansa sha’awar yadda Rarara ke kula da iyalinsa da kuma yadda yake hada zumunci da su ta hanyar irin wannan nishadi.





