Rashin jin daɗi yayin jima’i abu ne da yawanci maza da mata ke fuskanta. Amma ba koyaushe infection ne ke haifar da shi ba.
A mafi yawan lokuta, matsala tana cikin kwakwalwa, sha’awa, ko yanayin jiki da tunani.
Wannan labarin zai taimaka maka ka gane gaskiya daga ƙarya, da abubuwan da zasu iya kawo rashin jin daɗi yayin jima’i.
- Shin Infection Na Iya Haifar Da Rashin Jin Daɗi?
Eh, amma ba koyaushe ba. Infection yawanci yana kawo:
Zafi ko kaikayi a gaba
Zubar wani ruwa mai wari
Ƙuna yayin fitsari
Ciwo a maraina ko ciki
Idan baka da waɗannan alamun, mafi yawan lokaci ba infection ba ne. - Matsalolin Da Ke Haifar Da Rashin Jin Daɗi
a) Matsalar Kwakwalwa (Psychological)
Yawancin mutane suna sa ran jima’i zai zama kamar a fina-finai. Wannan:
Yana kawo tsoro ko damuwa kafin ko yayin jima’i
Yana sanya mutum ya yi nazari sosai kan kansa
Yana kashe jin daɗin yanayi
b) Rashin Dacewar Sha’awa (Libido Mismatch)
Sha’awa ba ta da ƙarfi a wannan lokaci
Mata ba sa jan hankalinka sosai
Gajiya, damuwa, ko rashin bacci na rage jin daɗi
c) Yawan Canza Mata
Rashin kusanci na zuciya da rashin soyayya na rage jin daɗi
Yin jima’i da yawa ba tare da haɗin kai na zuciya ba
d) Tasirin Kallo da Istimna’i a Baya
Idan mutum ya saba da kallon blue film ko yin istimna’i mai yawa, jiki na saba da irin stimulation ɗin
Wannan na sa jima’i na gaske ya zama “ba sosai ba” - Tambayoyi Masu Muhimmanci
Ka tambayi kanka:
A lokacin jima’i, azzakari yana tashi da kyau?
Kana kawowa lafiya?
Babu zafi, kaikayi, ko wari?
Idan amsoshin sun eh, lafiyar jiki tana da kyau, kuma matsalar ba infection ba ce. - Abin Da Ya Kamata Ka Yi
Kada ka sha maganin infection kai tsaye ba tare da gwaji ba – zai iya lalata jiki.
Idan kana shakka, yi:
Gwajin fitsari
Semen test
Duba STI
Kula da tunani da yanayin kwakwalwa:
Rage damuwa
Mai da hankali kan kusanci da soyayya
Inganta bacci da motsa jiki.
Rashin jin daɗi yana da mafita idan aka fahimci asalin matsalar.
Rashin jin daɗi yayin jima’i ba koyaushe infection ba ne. Mafi yawan matsalolin suna cikin tunani, yanayin jiki, ko rashin dacewar sha’awa.- Ka gane dalilinka, ka kula da lafiyarka, ka mai da hankali kan soyayya da kusanci, kuma ka nemi shawara daga likita idan bukatar hakan ta taso.






