Daren farko a gidan aure lokaci ne na musamman ga amarya da ango. Wannan dare ba na tsoro ko damuwa bane, sai dai lokaci ne na shaƙuwa, soyayya, da gina zumunci kafin ko bayan kusanci na aure.
Gudanar da wannan dare cikin natsuwa, fahimta da addu’a na da matuƙar muhimmanci ga ingantacciyar rayuwar aure.
Irin Saduwar Da Ya Kamata:
- Fara da Natsuwa Da Addu’a:
An so ma’aurata su fara dare da addu’a tare, domin neman albarka da rahamar Allah a sabuwar rayuwarsu.
- Jawabi Da Gaisuwa Mai Sanyi:
A ba juna lokaci su shaƙata, su fahimci juna, su tattauna cikin ladabi da kalmomin girmamawa da kwantar da hankali.
- Shiga Da Wasa Da Soyayya:
Ba lallai a fara da jima’i kai tsaye ba. Wasa, murza hannaye, shafa da rarrashi ba tare da gaggawa ko dole ba yana rage fargaba.
- Kula da Juna da Bukatun Jiki:
Kar a tilasta wani mataki duk da an shigo gida. Kowanne ya fahimci na dayan, a gudanar da duk wani abu ne bisa jituwa, yarda da kulawa.
- Tsafta:
A kula da wankan tsarki da kamshi a jiki. Tsabtar gado da muhalli na ƙara samar da kwanciyar hankali.
- Karancin Jima’i a Daren Farko:
Idan zuciya ko jiki bai shirya ba, ba dole bane a yi jima’i a daren farko. Girmama ji da yanayi abu ne mai kyau.
Abunda Yakamata Ku Sani:
Daren farko lokaci ne na sanin juna, fahimtar dabi’u, da ƙarfafa soyayya.
A shigo da hakuri, jituwa, da addu’a a cikin rayuwar aure tun farko. Idan aka fara da fahimta, za a sami kwanciyar hankali a rayuwar gida.






