Yin saduwa cikin gaggawa abu ne da wasu ke dauka al’ada, musamman a wasu yanayi. Sai dai, yin hakan na iya haifar da matsaloli ga lafiya, soyayya, da jin daɗin rayuwar ma’aurata.
Fahimtar illolin gaggawa wajen saduwa na taimakawa wajen inganta kusanci da zumunci.
Illolin Yin Saduwa Cikin Gaggawa:
- Bushewar Fata da Jin Ciwo:
Rashin shiri ko wasa kafin saduwa kan kawo bushewar fata, hakan yana haifar da jin ciwo ko rashin jin daɗi ga ma’aurata. - Konewar Jiki ko Karce Fata:
Gaggawar motsa jiki ba tare da natsuwa ko amfani da ruwa/mayin taimako ba, na iya jawo rauni ko karce a fata. - Rashin Jin Daɗin Saduwa:
Ba a kai matsayi na jin daɗi da gamsuwa, hakan kan sa ɗaya daga cikin ma’aurata ko duka su daina jin ƙaunar kusanci. - Ciwon Ciki ko Gabobi:
Rashin fara saduwa da wasa ko motsa sha’awa na iya jawo ciwon ciki ko gabobin jiki, musamman ga mata. - Yawan Sabani da Saurin Bacin Rai:
Gaggawa na kawo damuwa, sabani ko rashin fahimta a tsakanin ma’aurata saboda rashin natsuwa da kwanciyar hankali. - Ƙara Hatsarin Infection:
Gaggawar saduwa ba tare da tsafta sosai ba, na ƙara yiwuwar kamuwa da wasu cututtuka.
Jin daɗin kusanci da saduwa yana bukatar natsuwa, lokaci da fahimtar juna.
Kaucewa gaggawa na taimakawa samar da ƙauna, jin daɗi da lafiya a rayuwar aure.






