A Musulunci da kimiyya, tsabta na da matuƙar muhimmanci musamman bayan saduwa.
Jima’i ba wai kawai kusanci ba ne, akwai musayar ruwan jiki da ƙwayoyin cuta.
Idan ba a yi wanka da wuri ba, hakan na iya haifar da matsaloli ga lafiya da zamantakewar aure.
- Yawaitar Kwayoyin Cuta a Jiki
Bayan jima’i:
– zufa
– maniyyi
– ruwan farji
– ƙwayoyin fata
duk suna taruwa a jiki.
Idan ba a yi wanka ba, waɗannan sukan zama wurin kiwon ƙwayoyin cuta da fungi.
Wannan na iya haifar da: – kaikayi
– ƙaiƙayi
– wari mara daɗi
– ƙuraje a al’aura - Ciwon Sanyi da Cututtukan Fitsari
Rashin wanke al’aura bayan saduwa na iya sa ƙwayoyin cuta su shiga:
– mafitsara
– farji
– mazakuta
Wannan na iya haifar da: – zafi yayin fitsari
– yawan fitsari
– kaikayi a al’aura
– jin nauyi ko ƙuna
Mata sun fi fuskantar wannan matsala. - Wari Mara Daɗi a Jiki
Idan maniyyi ko ruwan farji ya bushe a fata:
yana canzawa ya zama wari.
Wannan na iya:
– rage sha’awar miji ko mata
– haifar da ƙyama
– rage jin daɗin aure - Zai Iya Jawo Rashin Jin Daɗin Saduwa a Gaba
Idan mutum yana yawan jin:
– kaikayi
– wari
– ƙuna
to jima’i zai zama: – wahala
– mara daɗi
– ba tare da sha’awa ba
Wannan na iya rage kusanci da soyayya. - Rashin Cika Tsarin Ibada a Musulunci
A Musulunci:
– sallah
– karatun Alƙur’ani
– kusantar masallaci
duk suna bukatar tsarki.
Idan ka yi jima’i ka ƙi yin wankan janaba:
ibadarka ba ta cika ba.
Wannan babban hasara ne ga aure da addini. - Zai Iya Jawo Ciwon Fata
Ragowar zufa da ruwan jima’i a fata na iya haifar da:
– fungal infection
– kurajen al’aura
– kumburi
– ja-ja a fata
Abin Da Ya Kamata A Yi Bayan Jima’i
Da zarar an gama:
A yi fitsari (musamman ga mata)
A wanke al’aura da ruwa
A yi wankan janaba da wuri
A canza kaya
A shafa turare ko man jiki
Wannan yana kare: – lafiya
– aure
– ibada
Kammalawa
Rashin wanka bayan jima’i ba ƙaramin abu ba ne.
Yana iya:
– lalata lafiya
– rage sha’awa
– kawo wari
– hana ibada
Tsabta bayan jima’i ibada ce da kuma kulawa da aure.






