Saduwa tsakanin ma’aurata abu ne da Allah Ya halatta kuma yana da muhimmanci wajen ƙarfafa dangantaka. Amma akwai wasu al’amura da suke faruwa a jikin mace waɗanda ke nuna lafiyarta da jin daɗinta.
Ɗaya daga cikin waɗannan shi ne ruwan jiki (lubrication) da yake fitowa daga mace lokacin saduwa.
Rashin wannan ruwa na iya haifar da matsaloli da dama.
Menene Kuka ko Ruwan Jiki?
Ruwan jiki (vaginal lubrication) wani ruwa ne da jikin mace yake samarwa ta hanyar ƙwayoyin halitta a cikin farjinta. Wannan ruwa yana taimakawa wajen:
- Sauƙaƙa shigar namiji
- Rage gogayya da zafi
- Kare bangon farji daga rauni
- Nuna cewa mace tana jin daɗi kuma jikin ta ya shirya
Illolin Rashin Kuka Ga Mace
1. Zafi da Rashin Jin Daɗi
Rashin isasshen ruwa yana sa saduwa ta zama mai zafi ga mace. Wannan na iya sa ta ji tsoro ko ƙyama ga saduwa gaba ɗaya.
2. Raunuka a Farji
Gogayya marar ruwa na iya haifar da ƙananan raunuka a bangon farji, wanda zai iya kawo:
- Kumburi
- Kamuwa da cututtuka
- Zubar jini kaɗan
3. Kamuwa da Cututtuka
Lokacin da farji ya samu rauni, sai ya zama sauƙi ga ƙwayoyin cuta su shiga, wanda zai iya haifar da:
- Infection
- Ƙaiƙayi
- Wari mara kyau
4. Matsalar Haihuwa
Rashin isasshen ruwa na iya shafar tafiyar maniyyi zuwa mahaifa, wanda zai iya rage damar samun ciki.
5. Matsalar Tunani da Dangantaka
Mace da ba ta jin daɗi ba za ta fara guji mijinta, wanda zai iya haifar da:
- Rashin fahimtar juna
- Tashin hankali a gida
- Rabuwa
Dalilin Da Yasa Mace Ba Ta Kuka
- Rashin foreplay (wasa kafin saduwa): Jikin mace yana buƙatar lokaci kafin ya shirya
- Damuwa ko Stress: Tunanin da yawa na iya hana jiki aiki yadda ya kamata
- Canjin hormones: Musamman bayan haihuwa ko lokacin menopause
- Wasu magunguna: Kamar maganin hana haihuwa
- Rashin sha ruwa: Dehydration na shafar samar da ruwan jiki
- Cututtuka: Wasu cututtuka na iya rage samar da ruwa
Maganin Matsalar
- Ƙara lokacin foreplay – Bai kamata a yi gaggawa ba
- Magana tsakanin ma’aurata






