Mata ku karanta wannan, banda maza
Kowanne dare yana da nasa sirrin kwanciya mai lafiya, kuma cire riga (bra) yayin bacci yana da fa’ida da yawa ga lafiyar nononki da jikinki baki ɗaya.
Ga wasu dalilai da yasa ya kamata ki cire bra lokacin da kike bacci:
1. Yana ba nononki hutu – Sanya bra a dare na matse nono, yana hana tsokar nono hutu.
Cire bra yana ba nononki damar hutawa da sake dawowa cikin siffarsa ta asali.
2. Yana sa ki yi bacci cikin nutsuwa – Rashin matsewa na taimakawa jikinki ya ji daɗi, hakan na sa baccinki ya inganta.
3. Yana rage zufa da ƙamshi mara daɗi – Idan kina sanya bra mai matsewa, musamman da dare, yakan haifar da zufa a ƙasan nono, wanda zai iya haifar da ƙamshi mara daɗi.
4. ✅ Yana ƙara soyayya – Idan kika kwanta ba tare da bra ba, hakan na kara jin daɗin masu kwanciya da ke gida, musamman maigida, saboda jin daɗin fata da siffa.
5. ✅ Yana taimakawa nonon ya tsaya cikin siffa – Rashin matsewa yana sa nono ya zauna cikin siffarsa na asali, ba ya lulluɓe ko lankwasa kamar an shango goro.
Don haka, lokacin dare, cire bra ki bawa jikinki “vacation.”
Wannan ba kawai don jin daɗi bane, har ma yana inganta lafiya da kwanciyar hankali. Lafiya tafi kyau da jin daɗi.
—






