Shugaban kwamitin kudi da sauye-sauyen haraji na tarayya, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa duk wani kudin da mata masu zaman kansu ke samu a Najeriya, wajibi ne a biya haraji akansa.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin fara karbar haraji daga duk wanikuɗaɗe da ake samu a kasar, ciki har da na mata masu zaman kansu.
Wannan sanarwar ta fito ne daga shugaban kwamitin kudi da sauye-sauyen haraji na tarayya, Taiwo Oyedele, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Taiwo Oyedele ya bayyana a wani faifan bidiyo da ya karade yanar gizo cewa, kowane kudi da mata masu zaman kansu ke samu wajibi ne a biya haraji a kansa, ba tare da la’akari da hanyar da aka bi wajen samun kudin ba.
Ya ce duk wannan na kunshe ne a cikin dokar da ta kafa tsarin biyan haraji a Najeriya.
A cewar Oyedele, gwamnati ta dauki wannan mataki ne don tabbatar da daidaito da kuma kara shigo da kudade cikin asusun kasar.
Wannan mataki zai shafi mata da ke gudanar da sana’o’i ko ayyuka masu zaman kansu, wadanda ba su karkashin wani kamfani ko gwamnati ba.






