A kokarin kare masana’antu da bunkasa tattalin arziki, gwamnatin tarayya ta shirya taron yaƙi da cin ganda a birnin Abuja, domin magance barazanar da ke shafar kamfanonin sarrafa fata da ake fitar wa ƙetare.
Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da babban taron yaƙi da cin ganda a Abuja, a sakamakon barazanar da aka gani na cin ganda da ke kawo cikas ga kamfanonin da ke sarrafa fata da niyyar fitar da su ƙetare don sayarwa.
Manufar taron ita ce fadakar da masu ruwa da tsaki kan illar cin ganda ga ci gaban masana’antu da yan kasuwa, tare da samar da dabarun da za su taimaka wajen inganta tsaro da amincin sana’a.
Masana da hukumomi sun yarda cewa ya kamata a hada kai don magance matsalar cin ganda, tunda tana iya haifar da raguwar samun kudin shiga da fitar da kayayyaki ƙasashen waje.

Leave a Reply