Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kwarin gwiwa kan yadda gwamnatinsa ta cika kashi 80 na duk alkawuran da suka dauka, a yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar badi a gaban majalisar dokoki.
A yau Laraba, Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya gabatar da kasafin kudin shekarar badi a gaban majalisar dokokin jihar.
Yayin gabatarwar, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cimma sauke nauyin kashi tamanin daga cikin dari na alkawuran da aka dauka wa al’ummar Kano.
Gwamnan ya ce: “Mun cimma sauke nauyi kashi 80 na alkawuran da muka dauka.
Wannan masu girma wakilai yana nuna irin kwazonta, jajircewa, da niyyar kawo canji a jihar Kano.”
Gwamna Abba ya kara jan hankali ga ’yan majalisar dokokin da su ci gaba da goyon bayan ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ke aiwatarwa, da fatan cewar shekarar badi za ta kasance cike da nasarori ga jihar Kano.
Wannan dai ya jawo martani daga jama’a wadanda ke kokarin ganin gwamnatinsa ta aiwatar da dukkan alkawuran da aka dauka, musamman kan inganta rayuwar al’umma, ilimi, lafiya da zaman lafiya a Kano.






