Yawanci samari suna damuwa ko suna zargi da matansu idan suka auri budurwa amma basu ga jinin budurci a lokacin saduwa ta farko ba.
Wannan ra’ayi ba daidai bane, kuma bai kamata ya zama hujja ta kiran mace ‘yar iska ba.
Menene Budurci?
Budurci wani fata ne dake cikin farjin mace matashiya.
Wannan fata ba mai kwari bane, kuma tana yagewa ne kawai lokacin da aka samu takura ko saduwa.
Hanyoyin Da Mace Ke Iya Rasa Budurcinta:
1. Saduwa da namiji
2. Daukar kaya mai nauyi
3. Guje-guje ko motsa jiki mai nauyi
4. Hawan keke
5. Hawan doki ko jaki
6. Mummunar faduwa
7. Sanya danyatsa a farji
8. Haihuwa
Wani lokaci fatar budurci bata yagewa lokacin saduwa ba, har sai lokacin haihuwa, wannan yana nuni da cewa jini ba shine ma’auni ba.
Muhimmancin Fahimtar Hakan ga Samari
Kada ka dauki matarka ‘yar iska ko mazinaciya idan baka ga jini ba lokacin saduwa ta farko.
Idan ka fara zargi kafin aure, hakan zai iya kawo matsala a zamantakewar aure.
Ya kamata ma’aurata su fahimci juna, su nuna girmamawa da yarda, ba tare da dogaro da jini a matsayin hujja ba.
Allah ya kiyaye mu da duk wani zargi mara tushe, ya basu mata nagari, ya bamu mazaje na gari, kuma ya albarkaci ma’aurata da zuria mai kyau.
Ameen.
—






