Da farko ya kamata ki gane cewa ke sabon shigace a saduwar aure bazaiyu kijin irin dadin da akeji ba na saduwa tinda har yanxu gaban bai gama zama dai daiba, sabida hanyar farjinki bata gama budewa ba shine yasa kikejin zafi, zaki daina jin daga sanda aka samu hanya sosai.
Amma kidinga shafa man zaitun yayin da zaku sadu, sanan bayan gama saduwa kidinga samu garin magarya, kanimfari, da lalle kina dafawa kina shiga zuwa minti 15.
Wanan farin ruwa mai kamar nono ba matsala bane, ba ma ko wacce mace take samun wanan darajar ba ta fitar ruwa mai kamar nono a lokacin da ake saduwa da ita, kuma sannan ruwan ni’ima ne da maziyyi da kuma maniyi suma sune hadewa subada wannan kalar ruwan, wanan kam kada ki damu lafiya ce.
Sanan wanan ruwan dake zuba yana bin jiknki shima ba matsala bane hakan yanuna mijinki yana da wadataccen miniyyi shine bayan gama saduwa yake dawowa kadan kadan sabida kinsan ba dukane yake zama a jikinkiba wanda ya ratsaki ya shiga mahaifa raguwar kuma zai fito idan kin tashi wani lokacin kuma wuni zakiyi ma yana zuba kadan-kadan yana bin cinyarki ko ya dinga zuba a pant dinki, duk ba damuwa kuma ba matsala bane.
Allah ta’ala yasa mu dace,ameen.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ






