Donald Trump Ya Gargadi Najeriya: “Za Mu Dau Mataki Mai Tsanani!” — Sabon Jawabi Kan Harin Kiristoci

Image result for Donald Trump Press Conference

shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake jaddada matsayinsa kan abin da yake faruwa ga Kiristoci a Najeriya. Trump ya ce lokaci ya yi da Amurka za ta dauki mataki mai tsauri. Wannan jawabi ya tayar da hankali a kafafen sada zumunta.

A wata hira da aka yi da shi, Trump ya bayyana damuwarsa kan yadda ake cin zarafi da kashe Kiristoci. Ya ce, “Idan Gwamnatin Najeriya ba ta dau mataki ba, Amurka za ta dau mataki mai tsanani. Ba za mu bari a ci gaba da zaluntar Kiristoci ba.”

Kalaman Trump sun jawo ce-ce-ku-ce a Duniya, musamman a shafukan sada zumunta inda mutane ke muhawara kan wannan mataki.

Kwararru a harkar diflomasiyya sun bayyana cewa irin wannan jawabi na matsa lamba kan Najeriya ya sanya Gwamnatin kasar ta kara kaimi don kare ‘yan kasa. A cewar Trump, “Amurka na bin dukkan hanyoyin diflomasiyya don kare wadanda ke cikin barazana.”

Ya kara da cewa, “Mun aika sako zuwa ga Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, cewa dole a kare kowane dan kasa, ba tare da wariya ba.”

Wannan irin sauti daga Donald Trump na kara jawo hankalin kungiyoyin kare hakkin dan Adam da Majalisar Dinkin Duniya, suna kira ga gwamnati da ta magance matsalolin kisan gillar da zalunci.

KALUBALE GA MAI KARATU:
Yawancin masu bibiyar lamarin na ganin cewa kiraye-kirayen duniya zai zamewa Najeriya alfanu, amma dole ne gwamnati tayi canji a cikin gida. Shin me kake tunani? Hadakar da Amurka zai kawo sauki ko kuwa cin fuska ne ga kasa?

Ka bayyana ra’ayinka a sashin comment, ka raba labarin, ka shiga muhawara a WhatsApp group din blog dinmu!

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *