Dalilin dayasa basir dinka yaki warkewa

  1. Rashin magance asalin matsalar

Basir yakan samo asali daga abubuwa kamar constipation (kashi mai tauri), yawan tari, wahalar yin fitsari,yawan zama ko tsayuwa. Idan baka gyara waɗannan, ko da an yi maganin basir, zai ci gaba da dawowa.

  1. Abubuwan da kake ci

Cin abinci mara fiber da rashin cin kayan lambu da ganye na sa bayan gida yayi tauri, wanda ke ƙara taazzara basir.

  1. Rashin shan ruwa isasshe

Jikin da bai samu ruwa ba yakan sa bayan gida yayi taurin gaske, wanda hakan yana ƙara taazzara basir.

  1. Zama tsawon lokaci a bayan gida

Yawan zama ko kallan waya a bayan gida na tsawaita matsin lamba akan jijiyoyin dubura. Wannan yana hana shi warkewa.

  1. Rashin motsa jiki

Zama da yawa a kujera ko gado ba tare da motsa jiki ba na hana jini zagayawa yadda ya kamata, hakan yana tsananta basir.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *