Dalilin dayakamata kasaka awara cikin jerin abincin dakake ci yau da kullum.

Awara na ɗaya daga cikin abinci a nan Arewa mafi ƙima amma mutane da yawa basu san muhimmancinta ba. Ga dalilin da ya sa, ya kamata ka saka awar a cikin jerin abincin ka na yau da kullum:

  1. Tana dauke da sinadarin furotin mai dinbin yawa (Protein):

– Awara tana ƙara ƙarfi, tana taimakawa tsokokin jiki, ƙashi, da jiki gaba ɗaya.
– Musamman ga masu cin abinci ba tare da nama ba, awara madadin nama ne.

  1. Ƙarancin mai da cholesterol:

– Tana rage haɗarin ciwon zuciya, hawan jini inji wasu bincike

  1. Tana ƙunshe da sinadarai masu hana ciwon daji (Isoflavones):

– Bincike ya nuna waken soya (wanda ake yin awarar ) na rage haɗarin kansar nono da prostate.

  1. Taimako wajen narkar da abinci:

– Awara bata da nauyi ga hanji, tana taimakawa masu fama da matsalolin ciki.

  1. Amfani ga ƙashi da hormones :

– Isoflavones a awara na taimakawa mata bayan sun shiga menopause wajen rage raunin ƙashi (osteoporosis).

Abun Lura:

– Kada ka yi amfani da mai mai yawa wajen soyawa, domin hakan zai rage fa’idarta.

Shin Kana cin awara a kai a kai? Ko kana ɗaukar sa kawai a matsayin abun kwadayi ne kawai bashi da wani amfani?

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *