Ɗan majalisa mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada a jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana manufar bidiyoyinsa da hotunan sa da suka karade shafukan sada zumunta, inda ya ce “saƙo ne ga abokan hamayyar siyasa” musamman maƙiyan sa.
A wata hira da gidan rediyon BBC sukayi dashi a Landan, Doguwa ya ce,
“Na zo Landan a daidai wata gaɓa da nake son na aika wa ƴan siyasa wani saƙo musamman maƙiyanmu da suka mayar da siyasa ta koma gaba da ƙiyayya. Musamman ƴan siyasar Doguwa da Tudun Wada waɗanda ke siyasa idanunsu a rufe.”

Alhassan Doguwa ya kara da bayyana cewa irin wannan walwala da hotuna da bidiyo da yake nunawa a Ingila, saƙo ne, yana yi ne don nuna wa Abokan siyasar sa da maƙiya cewa shi ne wakilin kowa a Doguwa, kuma matsayin sa na ɗan majalisa ba za a iya shafe shi ba; ko an ƙi da an so, Allah ya yarda. A cewar sa.
Ya ce, “Ina yin wadannan hotunan ne domin na yi walwala da nuna wa ƴan jihar Kano maƙiyana da wadanda suka fito daga Doguwa da Tudun Wada cewa ga ni dai wakilin Doguwa da Tudun Wada, to abu ne nake yi kamar wani cali-cali kuma saƙon ya je.”
Hashtags:
#AlhassanAdoDoguwa #KanoPolitics #Siyasa #London #BBCInterview #DoguwaTudunWada #LabaranHausa #ArewaPolitics
SEO Ideas / Keywords:

Leave a Reply