Wasu ma’aurata ko abokan zama suna fuskantar matsalar jin ciwo ko ɗaci lokacin saduwa. Wannan matsala na iya zama abin jin kunya, damuwa ko tsoro musamman ga wadanda ba su san dalilinta ba. Yin bincike da fahimta game da wannan lamari yana da matukar muhimmanci domin a ji daɗin saduwa da inganta zumunci.
Abubuwan Da Ke Iya Jawo Ciwo Lokacin Saduwa:
- Bushewar Fata (Rashin Isasshen Ruwa):
Ko mace ko namiji, idan babu isasshen ruwa a gabobi ko ake gaggawa wajen saduwa, hakan na haifar da jin ɗaci ko ciwo. - Infection Ko Rashin Tsafta:
Cututtuka kamar yisti (yeast infection), kwayar chlamydia, ko wata cuta a farji na iya jawo ƙaiƙayi da zafin saduwa. - Matsanancin Damuwa da Tsoro:
Idan mutum na da damuwa ko fargaba kafin saduwa, gaba zai kulle ko rawa, hakan kan haifar da ciwo ko rashin jin daɗi. - Karfi Ko Matsin Da Bai Dace Ba:
Yin amfani da ƙarfi sosai ko matsin da bai dace ba yayin saduwa na iya jawo radadi. - Canjin Hormon ko Illar Magani:
Wasu lokuta bayan haihuwa, yayin daukar magani ko canjin hormone na iya rage ruwa ko taushi a farji ko azzakari.
Yadda Za A Magance Matsalar Ciwo Lokacin Saduwa
- Dauki lokaci sosai wajen wasa da motsa jiki kafin saduwa.
- Kula da tsafta akai-akai.
- Yi saduwa a cikin natsuwa da fahimta, kada a matsa lamba.
- Nemi shawarar likita idan matsalar ta dade ko tana da alaka da rashin lafiya.
- Iya amfani da kayan lubricants idan an ga bukata.
Jin ciwo lokacin saduwa ba dole bane ya zama jiki ko dabi’a. Fahimta, natsuwa da tsafta su ne mabuɗin jin daɗi da samun lafiya lokacin kusanci. Kada a ji kunya ko tsoro wajen neman ilimi ko magani.
Ku cigaba da bibiyar jaridar Arewa Jazeera domin samun ingattatun rahotanni da sirrinkan ma’aurata.







Dalilin’saduwar’aure