Aure da jima’i mai daɗi yana buƙatar fahimtar juna da wasa cikin hikima.
Wasu maza suna yin kuskure na nuna rashin kulawa yayin saduwa da matansu, musamman idan suna fama da matsalar raunin gaba.
Me Ya Sa Romance Yake Da Muhimmanci
Romance ko wasa kafin saduwa yana taimaka wa mace wajen saurin kawo ruwa da jin daɗi lokacin ibada.
Ba wai kawai yana sa mace ta gamsu ba, har ma yana taimaka wa namiji wajen samun ƙarfin jiki da jin daɗi.
Misali:
Idan kai kana kawo ruwa cikin minti 5, ita kuma cikin minti 6, yin wasa da ita sosai kafin saduwa zai taimaka mata ta kawo ruwa a lokacin da ya dace.
Idan aka yi wasa da kyau, lokacin da kake cikin minti 3, zata kawo ruwa, kai kuma kana iya samun gamsuwa cikin minti 5.
Wannan yana nuna cewa wasan romance yana da tasiri sosai wajen daidaita gamsuwar ma’aurata.
Ba kawai yana kawo jin daɗi ba, har ma yana rage matsalolin raunin gaba da ciwon mara a mace.
Shawara Ga Maza
1. Kada ka yi gaggawa, ka fara da wasa da mata ka nuna kulawa da soyayya.
2. Ka fahimci yadda jikinta ke motsawa, kada ka matsa mata lamba.
3. Romance yana da muhimmanci fiye da yadda ake tunani; yana haifar da haɗin kai da jin daɗi ga ma’aurata.
Aure mai daɗi da gamsuwa baya ta’allaka ga saduwa kadai.
Wasa da romance kafin saduwa yana tabbatar da cewa kowa ya gamsu, kuma yana ƙara haɗin kai tsakanin ma’aurata.
—






